2 Satumba 2021 - 12:51
An Bukaci Gwamnatin Libya Ta Sallami Dukkan Mayakan Da Suka Shigo Kasar Daga Kasashen Waje

Taron kwanaki biyu na kasashe makobta ga kasar Libya ya bukaci gwamnatin rikon kwaryan kasar ta sallami dukkan mayakan da aka shigo da su kasar daga kasashen waje, sannan ta yi riko da yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya ta kasar wacce ta bukaci a gudanar da zaben manjalisar dokoki da kuma na shugaban kasa a cikin watan Decemba mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Shafin yanar gizo na labarai ‘Africanews’ ya kara da cewa ministocin harkokin waje na kasashen Cadi, Nijer, Tunisiya, Sudan, Masar da Aljeriya ne suka halarci taron na kwanaki biyu a birnin Aljies na kasar Aljeriya.

Har’ila yau, Jan Kubis wakilin MDD na musamman a kasar Libya da babban sakataren kungiyar kasashen larabawa Ahmed Aboul Gheit da kuma wakili daga kungiyar tarayyar Afrika ma sun sami halattan taron.

Tun shekara ta 2011 kungiyar tsaro ta NATO ta tallafawa yan tawaye suka kifar da gwamnatin Mu’ammar Kazzafi , wanda ya daga karshe ya kai ga barkewan yaki a kasar.

Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekarar da ta gabata, a lokacinda aka sasanta tsakanin mutanen kasar sannan aka kafa gwamnatin rikon kwarya.

342/